2 Maris 2022 - 17:27
Har Yanzu Tsugunne Ba Ta kare Ba Game Da Rikicin Shugabanci A Libiya

Majalisar dokokin Libiya ta amince da sabuwar gwamnati da Fathi Bachagha ke jagoranta, tare da bijire wa ta Abdelhamid Dbeibah da ke birnin Tripoli.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan na zuwa ne bayan da M. Dbeibah ya ki mika mulki cikin ruwan sanyi.

'Yan majalisa 92 ne suka kada kuri'ar amincewa da gwamnatin Fathi Bashagha daga cikin 101 da suka halarcin zaman a birnin Tobruk da ke gabashin kasar.

Wannan dai wata alama ce dake nuna har yanzu tsugunne ba ta kare ba game da rikicin shugabanci a wannan kasa ta Libiya.

A ranar 10 ga Fabrairun da ya gabata ne, majalisar ta Libiya ta nada Bachagha domin ya maye gurbin Dbeibah a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi, saidai firaministan dake ci ya yi fatali da hakan yana mai cewa ba zai mika mulki ba illa ga gwamnatin da aka zaba.

Libiya dai ta fada rikici ne tun bayan guguwar neman sauyin da ta yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar Muammar Ghaddafi a cikin shekarar 2011, kuma ta jima da take fama da irin wannan rikicin shugabanci.

342/